Kungiyar samar da wutar lantarki ta kasa tafa fara yajin aiki a Kano daga ranar yau Laraba
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Sakataren tsare-tsare mai kula shiyyar Arewa maso yammacin ƙasar nan, na ƙungiyar Kwamared Muhammad Babangida, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Jaridar Neptune Prime Hausa.
KU KUMA KARANTA:Ƙarancin wutar lantarki a Kano ya sa al’umma suna ta rubibin sayan ƙanƙara
Ya ce sun ɗauki wannan matakin ne sakamakon yadda suke zargin kamfanin KEDCO, da gaza bai wa ma’aikatan kuɗin Fanshonsu aƙalla na watanni Ɗari da suka gabata.
Kwamared Muhammad, ya kuma ce sun yi bakin ƙoƙarin su don ganin an biya ma’aikata haƙƙin nasu ma watanni ɗari, amma hakan ba ta samu ba, a don haka ne suka ɗauki gaɓarar tafiya yajin aikin.









