Tsohuwar Editar Neptune Prime Amina Alhassan ta rasu
Tsohuwar ‘yar jarida kuma tsohuwar edita, sannan babbar jami’i gudanarwa ta jaridar Neptune Prime, Hajiya Amina Alhassan, ta rasu. Ta rasu ne a ranar Talata a wani asibitin daji dake Legas bayan ta yi fama da cutar kansar Mama.
Wani ɗan’uwa, Ahmad Makama, ya fitar da labarin rasuwar ta a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 20 ga Mayu, 2025.
KU KUMA KARANTA:Mawallafin Neptune Prime zai ƙaddamar da asibitin cutar kansa, makaranta, da gidauniyar tallafi a Yobe
Amina, ‘yar tsohon jami’in Diflomasiyya, Ambasada Yahya Alhassan, an haife ta ne a ranar 27 ga Janairu, 1969, kuma ‘yar asalin Jihar Neja ce. Ita tsohuwar ɗaliba ce a Kwalejin ’Yan mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Bida, kuma ta yi karatu a Kuwait English School, Jami’ar Maiduguri, da Jami’ar Abuja.
Hajiya Amina ta yi shekaru masu yawa a harkar yaɗa labarai, tsohuwar editan Neptune Prime, wacce daga baya ta zama Babban Jami’in Kula da Kafafen Yada Labarai. Ta yi murabus ne a shekarar 2023 bayan wata ganawa da gwamnatin jihar Neja.
Amina kuma ta kasance tsohuwar Edita ta ƙarshen mako a jaridar LEADERSHIP kuma mamba a Hukumar Edita.
Za a yi jana’izar ta a yau (Laraba) da ƙarfe 2 na rana, bayan sallar Azahar a babban masallacin Abuja. Ta rasu tana da shekaru 56, ta bar ‘ya’ya huɗu, uwa da sauran ‘yan’uwa.