Kowane irin nau’in barasa na haifar da lalacewar zuciya, ƙoda da huhu – WHO

0
232
Kowane irin nau'in barasa na haifar da lalacewar zuciya, ƙoda da huhu - WHO

Kowane irin nau’in barasa na haifar da lalacewar zuciya, ƙoda da huhu – WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargaɗin cewa babu wani adadin barasa da ya dace a ce baya illa ga lafiya, inda ta tabbatar da cewa barasa na lalata zuciya da raunana kwakwalwa kuma na yin Illa ga hanta.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta gano wuraren da ake madara, barasa da lemo na bogi

WHO ta bayyana cewa barasa na cikin rukuni na farko na sinadarai masu haddasa cutar daji (Group 1 carcinogen), wato a rukuni ɗaya da taba sigari, kuma an tabbatar da cewa yana da alaƙa da aƙalla nau’o’in ciwon daji bakwai.

Bincike ya nuna cewa ko shan barasa kaɗan ko matsakaici na ƙara haɗarin cututtuka irin su ciwon zuciya, lalacewar hanta, damuwa da sauransu.

Likitoci sun ce ko dai mutum ya rage shan barasa ko ya daina gaba ɗaya, damar yin rayuwa mai tsawo da lafiya tana ƙaruwa tun daga rana ta farko.

Barasa tana lalata jiki daga kai har ƙafa. Yana sa kwakwalwa ta yi shiru ba tare da taimaka wa barci ba, yana ƙona ciki, yana ƙara hawan jini kuma yana jawo kumburi wanda zai iya haddasa daskarewar jini, bugun zuciya da bugun jini (stroke), inji masana.

Leave a Reply