No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kansa – Hafsan Sojin Najeriya

Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa ya shawaraci ‘yan Najeriya da su laƙanci dabarun kare kai daga haɗurra a matsayin mataki na ko-ta-kwana.

C.G Musa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels a ranar Alhamis.

Matsalar tsaro na addabar yankuna da dama na Najeriya, inda masu ɗauke da makamai ke kashe mutane tare da tarwatsa su daga muhallansu.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Katsina sun kashe masallata 13

Duk da cewa hukumomi na cewa suna bakin ƙoƙarinsu, amma lamarin na ci gaba da laƙume ɗaruruwan rayuka a yankunan da ake fama da irin waɗannan tashin-tashina, kamar arewa maso yamma da arewa maso gabas da kuma arewa ta tsakiyar ƙasar.

Lokacin da aka tambayi Christopher Musa kan ko ya kamata al’umma su koyi dabarun faɗa, ya ce “Ya kamata mutane su ɗauki wannan tamkar koyon tuƙi ne ko iyo, wannan abu ne da ake buƙata a rayuwa, ko da ana fama da yaƙi ko a’a”.

“Ina ganin ya kamata a wayar da kan kowane ɗan Najeriya kan tsaro a kowane mataki. Kare kai na da matuƙar muhimmanci,” in ji Musa.

KU KUMA KARANTA: An yi jana’izar mutane 15 da ‘yan bindiga suka kashe a Sakkwato

Ko a ranar Litinin, wasu mahara sun kashe masu ibada aƙalla 28 a wani masallaci da ke karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina, arewa maso yammacin ƙasar.

Haka nan a watan da ya gabata masu garkuwa da mutane sun yi wa mutum 38 yankan rago cikin waɗanda suke garkuwa da su a jihar Zamfara mai maƙwaftaka.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...