Kotun ɗaukaka ƙara a Kano za ta sanar da ranar yanke hukunci ga waɗanda ake zargi da kisan Hanifa

0
171
Kotun ɗaukaka ƙara a Kano za ta sanar da ranar yanke hukunci ga waɗanda ake zargi da kisan Hanifa

Kotun ɗaukaka ƙara a Kano za ta sanar da ranar yanke hukunci ga waɗanda ake zargi da kisan Hanifa

Daga Jameel Lawan Yakasai

Kotun Daukaka Kara dake zamanta a Sakatariyar Audu Bako, Kano, ta bayyana cewa za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci kan neman soke hukuncin kisa da aka yankewa Abdulmalik Tanko da Hashim Isiyaku.

Masu ƙara sun roƙi kotun da ta soke hukuncin kisa da Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke musu ta hanyar rataya, tare da sallamar su daga tuhumar.

Lauyan masu ƙara, Barista Attorney Eze Wike, ya nemi kotun da ta rushe hukuncin ƙasa gaba ɗaya tare da sallamar waɗanda ake ƙara.

Sai dai lauyan gwamnatin Jihar Kano, waɗanda ake ƙara, Barista Lamido Abba Sorondinki, yayi suka ga wannan buƙata, inda ya roƙi kotun da ta tabbatar da hukuncin kisa da Babbar Kotun Kano ta yanke.

KU KUMA KARANTA: Shari’ar Hanifa: Kotu ta yanke wa Tanko, tare da Hashim Isyaku hukuncin kisa

Alkalan kotun uku da suka saurari ƙarar Justice Moses Ugo, Justice O. O. Goodluck, da Justice A. R. Mohammed kuma sun bayyana cewa zasu sanar da ranar yanke hukunci a nan gaba.

Tun a shekarar 2022 Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 5 ta yanke musu hukuncin kisa bayan ta same su da laifi.

Leave a Reply