Shari’ar Hanifa: Kotu ta yanke wa Tanko, tare da Hashim Isyaku hukuncin kisa

0
264

Wata babbar kotun jihar Kano ta yanke wa Abdulmalik Tanko da Hashim Isyaku hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon samunsu da laifin yin garkuwa da kuma na kisan kai.

An gurfanar da Abdulmalik Tanko tare da wasu mutane biyu bisa zarge-zarge huɗu da suka haɗa da haɗa baki, garkuwa da mutane, tsarewa, da kuma kisan kai, wanda ya saɓawa sashe na 97, 274, 277, 221 na kundin laifuffuka na jihar Kano na shekarar 1991.

KU KUMA KARANTA: Shari’ar Hanifa: Kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta hanyar rataya

Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Usman Na’abba ya yanke hukuncin cewa lauyan da ke shigar da ƙara ya tabbatar da babu shakka cewa waɗanda ake tuhumar sun hada baki, sace tare da kashe yarinya ‘yar shekara biyar, Hanifa Abubakar.

Lauyan da ake ƙara, Barr Asiya Mohammed, tun da farko a madadin waɗanda aka yankewa hukuncin, ta roƙi kotun da ta yi musu adalci da jin ƙai.

Leave a Reply