Kotun ɗaukaka ƙara ta kori Muhammed Abacha a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano a PDP

Daga Saleh Inuwa,Kano

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Kano ta kori Mohammed Abacha, ɗan Sani Abacha, marigayi shugaban ƙasa, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar.

Jam’iyyar PDP ta gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna a jihar, wanda shi ne ya samar da Muhammed Abacha yayin da aka zaɓi Sadiq Wali a zagaye na biyu.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta amince da Wali a matsayin ɗan takarar gwamna kuma ya bayyana a jerin sunayen ‘yan takarar gwamna na hukumar.

Amma Muhammed Abacha ya shigar da ƙarar INEC a matsayin wanda ake kara na ɗaya, Wali a matsayin wanda ake ƙara na biyu, PDP na uku, da Wada Sagagi shugaban APC na Kano, a matsayin wanda ake ƙara na huɗu.

KU KUMA KARANTA: Muhammad Abacha ne ɗan takarar gwamna na PDP a Kano- Kotu

Bayan karar, a watan Disamba 2022, wata babbar kotun tarayya a Kano ta tabbatar da Muhammed Abacha a matsayin ɗan takarar gwamna.

Alƙalin kotun, Abdullahi Liman, ya soke zaɓen fidda gwanin da ya samar da Wali, inda ya ce halastaccen zaɓen shi ne ya samar da Abacha.

Daga nan ne alkalin ya umarci INEC ta amince da Muhammed Abacha a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Kano na PDP. Amma kotun ɗaukaka ƙara, a ranar Juma’a, ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun ta yanke, ta kuma ba da umarnin a amince da Wali a matsayin ɗan takarar gwamna.

Da yake yanke hukuncin baki ɗaya, kwamitin mutane uku ƙarƙashin jagorancin Usman Musale ya bayyana cewa Abacha ba shi da wani hurumin ƙalubalantar zaben fidda gwani da ya haifar da Wali tunda bai taɓa shiga aikin ba.

Idan dai za a iya tunawa, a jiya lokacin da dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ziyarci Kano domin yakin neman zaɓe, bai amince da ko ɗaya daga cikin ‘yan takarar gwamna 2 a jihar ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *