Kotun ɗaukaka ƙara ta kori ƙarar da NNPP ta shigar akan Doguwa

0
645

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Kano a ranar Juma’a ta yi fatali da ƙarar da jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) da ɗan takararta Salisu Yushau suka shigar a kan sake zaɓen Alhassan Ado Doguwa na jam’iyyar All Progressives Congress, (APC).

Doguwa yana wakiltar mazaɓar Doguwa da Tudun-wada a birnin tarayya. Kwamitin mutum uku ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Ita George-Mbaba, a cikin hukuncin da aka yanke, ya kuma yi watsi da ƙarar na rashin hurumin shari’a tare da tabbatar da hukuncin da kotun ta yanke.

Kotun dai ta amince da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta Majalisar Dokoki ta ƙasa da ta Jiha ta yanke. Mista George-Mbaba ya kuma yi watsi da addu’ar da masu ɗaukaka ƙara suka yi na hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa, (INEC), daga bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga Ado Doguwa tare da janye takardar shaidar da ta riga ta ba shi. Alƙalin ya kuma umurci masu ƙara da su biya waɗanda ake ƙaran kuɗi Naira dubu ɗari biyu (200,000) a matsayin kuɗin shigar da ƙara.

KU KUMA KARANTA: Shari’ar kisan gilla ba za ta iya hana ni tsayawa takarar Shugaban Majalisa ba – Doguwa

NAN ta ruwaito cewa kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta ƙasa da ta ‘yan majalisun jiha, a ranar 7 ga watan Afrilu, ta yi watsi da ƙarar da NNPP ta shigar na neman hana INEC gudanar da ƙarin zaɓe a mazaɓar Tudun Wada/Doguwa na tarayya a jihar.

Masu shigar da ƙara a ƙarar nasu na neman kotu ta yi watsi da hukuncin kotun da ta ce ba ta da hurumin dakatar da INEC daga gudanar da zaɓen. Waɗanda suka shigar da ƙara a cikin buƙatar nasu sun kuma buƙaci kotun da ta ajiye zaɓen ranar 15 ga watan Afrilu wanda ya bayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Tudun Wada/ Doguwa a birnin tarayya.

Waɗanda ake ƙara, a ƙarar su ne: Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, (INEC), Alhassan Doguwa, memba mai wakiltar Tudun Wada/ Doguwa Tarayya Kano da APC.

Tun da farko, Lauyan waɗanda suka shigar da ƙara, Adegboyega Awomolo, SAN, ya bayar da hujjar cewa sashe na 4 (6) na dokar zaɓe ta 2022 ya ba da ikon cewa kowace jam’iyya za ta iya ƙalubalantar hukuncin da INEC ta yanke, inda ya ƙara da cewa ɗaukaka ƙarar ta biyo bayan tanadin dokar zaɓe.

Ya buƙaci kotun da ta ba da damar ɗaukaka ƙarar sannan ta yi fatali da rashin amincewar waɗanda ake ƙara na farko. Lauyan wanda ake ƙara na farko, Idris Yakubu, ya buƙaci kotun da ta yi watsi da ƙarar.

Lauyan waɗanda ake ƙara na biyu da na uku, Nureini Jimoh da Abdul Adamu-Fagge, sun buƙaci kotun da ta yi watsi da babbar ƙarar da ke gaban kotun tare da yin watsi da ɗaukaka ƙarar da kuɗi.

Leave a Reply