Kotun Ƙolin Amurka za ta yanke hukunci kan takarar Donald Trump

0
221

Kotun ƙolin Amurka ta amince za ta yanke hukunci cewa ko ya dace a hana tsohon shugaban ƙasar Donald Trump tsayawa takarar shugaban ƙasar.

Jihohi biyu na Amurkar ne zuwa yanzu suka cire sunansa daga takardar zaɓen fid da da gwani, bisa dalilinsu na cewa a matsayinsa na mai tayar da zaune tsaye, ƙundin tsarin mulkin ƙasar ya haramta masa tsayawa takara.

A halin dake ciki kuma Shugaban Amurka Joe Biden ya yi jawabin yaƙin neman zaɓensa na farko a shekaran nan, inda ya yi mummunar suka kan Donald Trump, yana mai gargaɗin cewa tsohon shugaban na son yin amfani da tashin hankalin siyasa don cimma burinsa.

Ana ganin wannan shari’a za ta iya kasancewa ɗaya daga cikin mafiya ɗaukar hankali da kasancewa zakaran-gwajin dafi a siyasance a tarihin kotun ƙolin Amurka.

Donald Trump ya garzaya gabanta ne domin ta yanke hukunci kan cewa ko ya cancanta ya tsaya takarar shugabancin ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Amurka na son ci gaba da ƙawance da Nijar kan tsaro da haɗin kai

A watan da ya gabata ne jihohi biyu na ƙasar, Colorado da Maine, suka yanke hukuncin haramta wa tsohon shugaban na Amurka tsayawa takara a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyarsa ta Republican.

A bisa tanadin ƙundin tsarin mulkin Amurka, duk wanda ya kasance ɗan tawaye ko ya yaƙi hukuma to ba zai rike wani muƙami ba.

A kan hakan ne jami’an jihohin biyu suka ce ya haramta Trump ya nemi wani muƙami saboda rawar da ya taka a kutsen da aka yi wa zauren majalisun dokokin Amurka shekara uku da ta wuce.

To amma jami’ai a wasu jihohin basu yarda da hakan ba, suka kuma soko matakin hana shi takarar a matsayin wanda ya saba wa dumukuradiyya.

Ana ganin hukuncin da kotun ƙolin za ta yanke kan wannan batu zai iya haifar da wasu batutuwan ga gwagwarmayar zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a watan Nuwamba, kuma duk yadda ya kasance zai sa a zargi alkalan kotun da goyon bayan wani ɓangare.

Donald Trump ya kasance babban abin da Shugaba Biden ya mayar da hankali a kansa a jawabinsa na farko na yakin neman zaɓe na shekara.

A jawabin wanda ya gabatar a Pennsylvania, ɗaya daga cikin jihohi mafiya muhimmanci a zaɓen shugaban ƙasar wadda kuma ya samu nasara a 2020, ya yi gargaɗi na gaske kan haɗarin da ya ce dumukuraɗiyyar Amurka na ciki saboda Trump wanda y ace zai yi wa dumukuradiyya karan-tsaye domin kawai ya samu mulki.

Biden ya yi jawabin ne a jajiberin shekara uku da kutsen da magoya bayan Trump suka yi wa zauren majalisun dokokin Amurka, Capitol, don neman sauya sakamakon zaben 2020.

Mista Biden ya ce ba za lamunta da tashin hankalin siyasa ba a Amurka inda ya ce:

”Gungun Trump ba masu zanga-zangar lumana ba ne, tarzoma ce, ‘yan tawaye ne, ba masu kishin ƙasaba ne. Ba su mutunta kundin tsarin mulki ba. Sun je ne domin su watsa tsarin mulki. Trump ba zai yi abin da Shugaban Amurka ya wajaba ya yi ba.”

Sai dai yayin da Shugaba Biden ɗin ke ƙaddamar da yakin neman zaɓensa, alkaluman baya-bayan nan na ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ba abin da zai so ba ne domin kusan kashi 70 cikin ɗari na Amurkawa na ganin a shekara 81 ya yi tsufa ainun ya zama shugaban ƙasa.

Leave a Reply