Kotun majistray me lamba 90 dake zaman ta a madobi ƙarƙashin Jagorancin maishari’a Haj. Nadiya Ado Sake, ta ɗaure wasu mutane guda biyu inda ake tuhumar su da laifin haɗin kai da ta’ammali da tabar wiwi wanda ya haɗa da Ilyasu Idris mai shakaru 82, da Yakubu Ɗalha 35.
Bayan karanta masu ƙunshin tuhumar su ne, suka amsa nan take, nan kotu ta karanto musu hukunci inda ta ɗaure malam ilyasu Idris mai shekaru 82, tsahon makwanni uku babu zaɓin tara, akan laifin haɗa kai wanda mai sharia ta duba tsufan sa da kuma rokon da ƴaƴansa da kuma shi kansa yayi a gabanta na neman afuwa da sassauci, sannan kuma akan tuhumar samun su da tabar wiwi kimanin ɗauri 95 ta kuma ɗaure shi wata shida ko zaɓin tara ta 50,000.
Mai Shari’a Nadiya ta kuma aike da abokin hulɗar tasa Yakubu Dalha gidan gyaran hali na tsahon shekara ɗaya babu zaɓin tara, akan laifin haɗa kai kuma an ɗaure shi wata 6 ko zaɓin tarar dubu hamsin.
Mai shari’ar ta hana zaɓin tarar ne kasancewar wannan ba shine karo na farko da jami’an tsaro ke gurfanar dasu don girbar abunda suka shuka ba.
KU KUMA KARANTA: Da Ɗumi-ɗumi: Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamna Fintiri na Adamawa
Daga karshe Mai sharia tayi musu gargaɗi na su zama mutanan kirki kuma su ɗauki alkawarin daina saida kayan maye a wannan yanki na madobi jahar kano baki ɗaya.