Kotu ta yankewa matasa biyu hukuncin kisa bisa kashe ma’aikacin jami’ar Northwest a Kano

0
123
Kotu ta yankewa matasa biyu hukuncin kisa bisa kashe ma'aikacin jami'ar Northwest a Kano

Kotu ta yankewa matasa biyu hukuncin kisa bisa kashe ma’aikacin jami’ar Northwest a Kano

Babbar Kotun Jihar Kano dake zamanta a Miller Road, karkashin jagorancin Mai Shari’a Fatima Adamu ta yanke hukuncin kisa Aliyu Usaini Sheka da Amir Zakariyya Shamak hukuncin kisa bisa kashe wani ma’aikacin jami’ar Northwest da ke jihar Kano.

Freedom Radio ta rawaito cewa tunda fari an gurfanar da Aliyu Usaini Sheka da Amir Zakariyya Shamaki bisa tuhume-tuhumen hadin baki domin aikata laifi, fashi da makami, da kuma kisan kai.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta umarci Hisbah ta ɗaura wa Ashiru Mai Wushirya aure da ‘Yar Guda nan da kwanaki 60

A zaman kotun na yau Litinin, lauyan gwamnati kuma mai gabatar da ƙara, Barista Lamido Abba Sorandinki, ya gabatar da shaida uku, sai kuma wadanda ake tuhuma suka kare kansu.

Kotun ta same su da laifi, inda ta yanke musu hukuncin daurin shekaru 5 bisa laifin haɗin baki domin aikata laifi, sai kuma shekaru goma a laifin fashi da makami, sannan a laifin kisan kai, kotu ta ce a kashe su ta hanyar rataya.

Wadanda ake tuhuma sun kashe ma’aikacin Jami’ar North West ne bayan sun yi masa fashin waya a ranar 11 ga Yuni, 2025.

Leave a Reply