Mai shari’a Ibironke Harrison na wata babbar kotun jihar Legas ta yanke wa ɗan sanda ASP Drambi Vandi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe lauya, Barista Bolanle Raheem.
Vandi ya harbe Misis Raheem har lahira a gaban mijinta yayin da take dawowa daga coci a ranar Kirsimeti 25 ga Disamba, 2022 a wani shingen bincike na ‘yan sanda a Legas.
Da take yanke hukunci a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba, kotun ta samu mataimakin Sufeton ‘yan sandan da aka dakatar da laifin kashe lauyan ranar Kirsimeti ta kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
An gurfanar da Mista Vandi a gaban kotu a ranar 16 ga watan Janairun 2023, kan zargin kisan kai amma ya ƙi amsa laifinsa. Kotun ta ba da damar ci gaba da sauraron ƙarar.
KU KUMA KARANTA: Kotu ta yankewa shugaban Kiripto hukuncin ɗaurin shekaru 11 a gidan yari
Gwamnatin jihar Legas ta ce Vandi ya harbe Misis Raheem a ƙirji a ranar 25 ga Disamba, 2022, a Ajah Roundabout, kan titin Lekki- Expressway, jihar Legas. Gwamnatin jihar ta shaida wa kotun cewa laifin ya saɓa wa sashe na 223 na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015.