Wata babbar kotu da ke zamanta a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin rai da rai.
Kotun dai ta samu mutumin ne mai suna Jide Afolayan Sunday mai kimanin shekara 33 da haihuwa ne dai laifin watsa wa budurwarsa ruwan batir.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Blessing Egwu, ta ce kotun ta samu wanda ake zargi ake ƙara da aikata laifin yunƙurin kisan kai ta hanyar watsa wa budurwarsa mai suna Glory Sylvester Ita ruwan gubar ne saboda ta ƙi auren shi.
Kazalika, kotun ta ƙara masa da tarar Naira milyan 10 domin ayi wa budurwar tasa tiyatar fuskarta da fatar jikinta .
Afolayan Sunday dai zai yi zaman waƙafi na rai da ran ne a gidan gyaran hali da ke Kalaba ne.
KU KUMA KARANTA: Kotu ta kori Gabriel Suswam a matsayin Sanatan Benuwe
Mai Shari’a Egwu ta ce wanda ake zargi a abin da ake zargin ya yi yunƙurin aikata kisan kai ba da wata ƙwaƙƙwarar hujja ba.
’Yan sanda sun kuma tuhumi mutumin da yaudarar yarinyar zuwa wani otel da ke unguwar Marian a ƙaramar Hukumar Birnin Kalaba, da zummar za su yi hira, amma ya ɓige da watsa mata gubar.
Sun kuma ce hakan ya sa gubar ta lalata mata yatsu da fuskarta har zuwa gadon bayanta.
Ɗan sandan ya ci gaba da cewar, “Saboda zafin asid din, ɗaya daga cikin kunnuwanta ya samu matsala ta kurumta.
“Lokacin da aka kama shi ya musanta aikata laifin, amma da aka zurfafa bincike an gano shi ne wanda ya watsa mata asid ɗin.”