Kotu ta umarci ‘yansanda su binciki Abdullahi Abbas kan zargin kalaman ɓatanci ga al’ummar Fagge

0
202

Kotu ta umarci ‘yansanda su binciki Abdullahi Abbas kan zargin kalaman ɓatanci ga al’ummar FaggeKotu ta umarci 'yansanda su binciki Abdullahi Abbas kan zargin kalaman ɓatanci ga al'ummar Fagge

Babbar Kotun Majistare mai lamba 5 da ke Court Road, Kano, ta ba da umarni ga Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kano da ya gudanar da bincike kan Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na Kano bisa zargin yin kalaman ɓatanci , tunzuri da kuma maganganun da ka iya haifar da kiyayya tsakanin al’umma, musamman a yankin Fagge.

Fitaccen lauya mai rajin kare ƴancin dan adam, Abba Hikima ne ya baiyana hakan a shafin sa na Facebook.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta aikewa Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki sammaci bisa zargin ɓatanci ga gwamnan Kano

Ya ce masu shigar da ƙorafin sun hada da wasu fitattun malamai, ‘yan kasuwa da shugabannin al’umma, wadanda suka zargi Abbas da yin maganganu masu cike da raini da tunzuri ga mazauna Fagge.

A cewar su, an ji Abdullahi Abbas a yayin wani taro yana alakanta mazauna yankin Fagge da rashin tarbiyya da daraja, tare da yin wasu kalamai da suka nuna tsageranci da raina doka, kamar yadda ya saba a lokuta da dama.

Leave a Reply