Kotu ta tsare wata matar aure a gidan gyaran hali kan zargin kashe jaririn kishiyarta ta hanyar shayar da shi maganin ƙwari a jihar Kano.
Kotu ta tisa ƙeyar wata matar aure zuwa gidan yari kan zarginta da kashe jaririn kishiyarta a Jihar Kano.
Mai shari’a Zuwaira Yusuf Ali na Babbar Kotun jihar Kano Mai lamba 16 ne ya ba da umarnin bayan gurfanar da matar auren daga ƙaramar Hukumar Ƙunci bisa zargin kisan jaririn.
KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure mutumin da ya damfari surukarsa akan zai saka Buhari ya aureta
Mai gabatar da ƙara, lauyan gwamnatin jihar, Barista Abba Lamiɗo Soronɗinki ya shaida wa kotun cewa matar ta kashe jaririn ɗan kimanin kwana 18 ne ta hanyar shayar da shi maganin ƙwari, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Bayan sauraron jawabin, alƙalin kotun, Mai shari’a Zuwaira Yusuf Ali ta bayar da umarnin tsare wacce ake zargin a gidan yari har zuwa ranar 2 ga watan Disamba 2023 don ci gaba da sauraren shari’ar.