Kotu ta sanya ranar fara sauraren shaidu kan kisan Nafiu

0
6
Kotu ta sanya ranar fara sauraren shaidu kan kisan Nafiu

Kotu ta sanya ranar fara sauraren shaidu kan kisan Nafiu

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Wata babbar kotun jahar Kano , ta sanya ranar 27 da 28 ga watan Janairun 2025, don fara sauraren shaidu kan tuhumar da ake yi wa, Hafsat Surajo ( Chuchu ) da kuma mijinta Dayya Abdullahi, da kashe Nafi’u hafiz, zargin da suka musanta.

A zaman kotun lauyar gwamnatin Kano, kuma mai gabatar da kara, Barista Halima Yahuza Ahmed, ta sake gabatar da kanta da kuma wadanda ake tuhumar, harma ta roki kotun, ta ba su wata rana don fara gabatar da shaidunsu, kuma kotun ta amince da rokon.

KU KUMA KARANTA:Kisan Nafi’u: An sake gaurfanar da Hafsat Chuchu a gaban wata kotun

Idan ba a manta ba tun a ranar 27 ga watan Disamban 2023 , rundunar yan sandan jahar Kano, ta gurfanar da Hafsat Surajo da kuma mijinta a gaban kotu.Alkalin kotun mai shari’a Justice Faruk lawan , ya sanya ranar 27 da 28 ga watan Janairun 2025, don masu gabatar da kara su fara gabatar da shaidunsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here