Kotu ta raba auren ‘yar Ganduje da ya shafe shekaru 16

2
308

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano a ranar Alhamis ta raba auren Asiya Ganduje, diyar Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, mai shekara 16.

Asiya ta garzaya kotu tana neman a raba aurenta da mijinta, Inuwa Uba, saboda ta gaji ta da zaman aure wanda suke da ‘ya’ya huɗu.

Alkalin kotun, Khadi Halliru Aliyu ya raba auren ne a lokacin da yake yanke hukunci kan lamarin a ranar Alhamis.

Sai dai Khadi Aliyu ya umarci diyar Ganduje da ta mayar wa mijinta Uba, sadakin N50,000 a matsayin kul’i.

KU KUMA KARANTA:‘Yar Ganduje ta sha alwashin mayar da sadakinta N50,000 da mijinta ya bayar na aurenta

Kotun ta kuma yi watsi da bukatar mijin Asiya na neman takardun kadarorin da ya ce nasa ne.

Lauyan mai ƙara Ibrahim Nassarawa, ya ce kotun ta yanke hukuncin ne bisa abin da ya ke na shari’ar muslinci tushen auren wanda shi ne sadaki.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Lauyan maigidan Umar I. Umar ya ce za su yi nazari kan hukuncin kuma za su jira mataki na gaba daga wanda yake karewa kan ko za su kai ga kotun daukaka kara a kan lamarin ko a’a.

Ya ce sun yi iya kokarinsu wajen daidaita ma’auratan amma abin ya ci tura musamman yadda ta haifa masa ‘ya’ya huɗu amma abin bai yiwu ba.

2 COMMENTS

Leave a Reply