Kotu ta raba auren wata 10 ta hanyar “Khul’i”

0
201

Wata kotu mai daraja ta ɗaya da ke Kubwa, Abuja, ta raba auren wata 10 da aka yi tsakanin wata ma’aikaciyar gwamnati, Wasilat Saka da mijinta, Tajudeen Jimoh, ta hanyar “Khul’i”.

Khul’i wata hanya ce da mace za ta iya rabuwa da mijinta a Musulunci, ta hanyar mayar da sadaki da duk abin da ta samu a lokacin rayuwarsu tare, ko kuma ba tare da mayar da komai ba, kamar yadda ma’aurata ko alƙali suka yi ittifaƙi.

Alƙalin kotun, Ibrahim Rufa’i, ya raba auren ne a bisa tsarin shari’ar Musulunci, bayan da Saka ta yi addu’ar sakin aure ta hanyar khuli bisa dalilin rashin soyayya da rashin so.

Rufa’i ya umarci Saka da ta mayar wa Jimoh sadakin Naira 50,000 sannan ta yi “Iddah” na wata uku kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kafin ta sake yin wani aure.

Ya ce Jimoh ya ƙi bayyana gaban kotu sau ɗaya tun da aka gabatar da ƙarar a watan Yuni kuma bai aika da wakili a kotun ba.

KU KUMA KARANTA: Ta roƙi kotu ta raba aurensu, saboda rashin kulawa daga mijinta

Ya ƙara da cewa mai gabatar da ƙara na kotu, Mista Dangana Bawa ne ya miƙa wa Jimoh da kansa, wanda ya miƙa wa kotun shaidar hidima.

Tun da farko Saka ta shaida wa kotun cewa ta auri Jimoh ne bisa tsarin shari’ar Musulunci a shekarar 2022, inda ta ƙara da cewa auren bai haifar da ‘ya’ya ba.

Sai dai ta shaida wa kotun cewa ita ba ta da sha’awar auren, inda ta roƙi kotun da ta raba auren a kan rashin son juna da kuma rashin jituwar da ba za a iya sasantawa ba.

“Ina roƙon kotu ta raba aurena ta hanyar “Khuli”, a shirye nake in mayar wa wanda ake ƙara sadakinsa Naira 50,000,” inji ta.

Leave a Reply