Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, ta kori tsohon gwamnan Jihar Benuwe, Gabriel Suswam daga Majalisar Dattawa.
Kotun a wani mataki na bai ɗaya da wasu alƙalai uku suka yanke a ranar Laraba, ta ce ta gamsu da cewa Suswam ba shi ne ya lashe zaɓen Sanatan Benuwe ta Arewa Maso Gabas a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kotun ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar Benuwe, wadda ta tabbatar da Suswam na jam’iyyar PDP a matsayin Sanata, bayan ta soke nasarar Mista Emmanuel Udende na jam’iyyar APC.
A cewar kotun ɗaukaka ƙarar, an yi kuskure a hukuncin baya wajen tantance shaidun da jam’iyyun suka gabatar a gabanta.
Don haka, kotun ta yi watsi da hukuncin kotun, inda ta ce ƙarar da ɗan takarar APC ya shigar a gabanta ta cancanta.
“Kotun sauraron ƙararrakin ta yanke hukunci a zaɓe ranar 8 ga watan Satumba, 2023.
KU KUMA KARANTA: Kotu ta bada umarnin gurfanar da tsohon shugaban KASCO kan zargin damfarar naira biliyan huɗu
“An dawo da wanda ya shigar da ƙara a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Benuwe ta Arewa maso Gabas da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.”
Idan dai ba a manta ba, Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) ta bayyana Udende a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan bayan ya samu ƙuri’u 135,573, inda ya doke Sanata Suswam wanda ya samu ƙuri’u 112,231.
Bayan rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen, Suswam ya garzaya kotu.
A hukuncin da kotun ta yanke, ta ce Suswam ya samu nasarar kafa hujjar cewa an tafka kura-kurai a ƙananan hukumomi biyar cikin bakwai na gundumar da aka yi zaɓen.
Kotun ta soke ƙuri’u 51,895 da Sanata Udende ya samu, sannan ta soke ƙuri’u 21,229 da aka kaɗa wa Sanata Suswam.
Bayan rage ƙuri’un da aka kaɗa, Sanata Suswam ya samu ƙuri’u 90,590 yayin da Sanata Udende ya samu ƙuri’u 82,699.
Da yake tabbatar da ƙarar, mai shari’a Ori Zik-Ikeoha ya jagoranci kwamitin yanke hukunci a kan Suswam, inda suka yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi a baya.









