Kotu ta ci tarar bankin Zenith miliyan 85 kan rufe asusun kwastoma

0
152
Kotu ta ci tarar bankin Zenith miliyan 85 bisa rufe asusun kwastoma ta hanyar amfani da takardar kotu ta bogi

Kotu ta ci tarar bankin Zenith miliyan 85 kan rufe asusun kwastoma

Daga Jameel Lawan Yakasai

Wata Babbar Kotun Abuja ta ci tarar bankin Zenith Naira miliyan 85 kan rufe asusun wani kamfani mai suna Abhulimen & Co ta hanyar amfani da takardar umarnin kotu ta bogi.

Mai shari’a S.U. Bature ya yanke hukuncin cewa bankin ya yi sakaci da bin doka bayan ya jingina da umarnin wata kotun Majistare da ke Mararaba Gurku, Jihar Nasarawa, wacce ba ta da hurumin yanke irin wannan hukunci.

KU KUMA KARANTA: An yi kira ga kotun ƙoli ta gaggauta yanke hukunci kan shari’ar masarautar Kano

Kotun ta umurci bankin da ya gaggauta bude asusun da kuma buga takardar neman afuwa a jaridu biyu na kasa da kuma a shafinsa na intanet. Haka kuma, kotun ta umarci bankin da ‘yansanda su biya diyyar Naira miliyan 60 da kuma Naira miliyan 25 a matsayin kuɗin shari’a.

Mai shari’a Bature ya bayyana cewa gaza sanar da mai asusun game da rufe asusun ya sabawa nauyin kula da abokin hulɗa da bankin ke da shi, kuma hakan ya nuna sakaci da rashin bin doka.

Leave a Reply