Kotu ta bada umarnin gurfanar da tsohon shugaban KASCO kan zargin damfarar naira biliyan huɗu

Gwamnatin jihar Kano ta tuhumi tsohon babban jami’i kuma manajan darakta na kamfanin samar da noma na jihar, (KASCO), Bala Muhammad Inuwa, da Ɗansa tare da wasu mutane biyu kan laifin zamba sama da naira biliyan huɗu.

Ofishin babban lauyan jihar Kano, kuma kwamishinan shari’a ne ya shigar da ƙarar da ake tuhumarsu, biyo bayan binciken da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ke yi.

Hukumar ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa waɗanda ake tuhumar sun karkatar da sama da Naira biliyan huɗu daga asusun kamfanin samar da noma na jihar zuwa asusun sirri.

An fara gabatar da ƙarar ne a kotu a ranar 6 ga watan Agusta, 2023 An kuma miƙa ta ga wani alƙalin babbar kotun jihar Kano, Hafsat Sani.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *