Kotu ta ɗaure mutumin da ya damfari surukarsa akan zai saka Buhari ya aureta

0
277

Wata kotun majistare a Minna da ke Jihar Neja ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗauri na shekara guda bisa zargin damfarar surukarsa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Malam Gambo Adamu ya riƙa shaida wa surukarsa cewar yana shirya aure tsakaninta da tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Surukar ta sa, Sa’adatu Aliyu wadda bazawara ce ta garzaya kotu ne tare da koken cewa surukin nata ya yi mata wala-wala bayan karɓar kuɗin da suka kai naira miliyan biyar daga hannunta da sunan zai haɗa aure tsakaninta da tsohon Shugaban ƙasar.

Ta ƙara da cewa, mai laifin ya kuma buƙaci ta kafa wata ƙungiya mai zaman kanta wadda za ta zama shugaba yayin da shi kuma surukin zai yi aiki a matsayin kakakin ƙungiyar, inda ya yi mata alƙawarin cewa za ta samu tallafi daga Gwamnatin Tarayya da ta jihohi, baya ga kujerun aikin Hajji.

KU KUMA KARANTA: Wata ‘yar sanda ta roƙi kotu ta raba aurenta, saboda yawan duka daga mijin

Ta shaida wa kotu cewa wata rana Gambo ya kai mata naira 100,000 a matsayin sadakinta, da huhun goro ɗaya da kuma soyayyiyar kaza da nufin cewa kyauta ce daga tsohon shugaban ƙasar, bayan ya yi mata ƙaryar ɗaura auren.

Ta ce a matsayinta na Amarya, ta yi ta dakon sabon angon nata ya zo ya ɗauketa.

Yayin da ba ta ganshi ba ne ta yanke shawarar kai surukin nata gaban kotun domin ta shiga tsakaninsu.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Musa Zago, ya ɗaure surukin nata wata 12 a gidan yarin, da zaɓin tarar naira 100,000, saboda samunsa da laifin yaudara, laifin da ya saɓa da sashe na 322 na kundin final cod.

Haka kuma, kotun ta umarci Malam Gambo ya biya surukar tasa naira miliyan biyu a matsayin diyya.

Leave a Reply