Kotu ta ɗaure matashi wata 6 kan satar magi da sabulu

0
204

Wata kotu da ke zamanta a garin Jos a Jihar Filato ta yanke wa wani matashi mai shekara 22 hukuncin ɗaurin wata shida a gidan yari bisa laifin satar kwalin magi da kuma kwalin sabulun Dudu-Osun da kuɗinsu ya kai N55,000.

Alkalin kotun, Shawomi Bokkos, ta yanke wa matashin hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa tare da rokon kotun da ta yi masa sassauci.

Ta kuma bai wa mai laifin zaɓin biyan tarar N20,000.

Tun da farko, ɗan sanda mai shigar da ƙara, Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa wani Mista Gbenga Ayantola ne ya kai kara ofishin ’yan sanda na “A” a ranar 10 ga watan Oktoba.

Ya ce wanda ake tuhumar ya kutsa cikin shagonsa inda ya saci katon na magi da kuma sabulun wanka waɗanda kudinsu ya kai N55,000.

Ɗan sandan ya shaida wa kotun cewa a lokacin da ’yan sanda ke gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

Ya ce laifin ya ci karo da dokar ‘Penal Code’ na laifuka.

Leave a Reply