Kotu ta ɗaure matashi wata 4 kan satar doya

0
239

Wata kotu da ke unguwar Dei-Dei a Abuja ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 22 hukuncin ɗaurin wata huɗu a gidan gyaran hali kan laifin satar doya a wata gona.

An tuhumi Adams wanda ba shi da laifin zamba da kuma sata.

Lauyan mai gabatar da ƙara, Mista Chinedu Ogada, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Oktoba, 2023.

Ogada ya ce, ’yan sandan da ke sintiri ƙarƙashin jagorancin Mista Tonushi Chibwa ne suka kama wanda ake tuhumar a tashar Dutsen Alhaji.

Ya ce a wannan ranar da misalin karfe 10 na dare rundunar ta kama mai laifin tare da wata tarin doya da ake zargin na sata ne.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ci tarar Gwamnan Kano N25m kan zargin Alhassan Doguwa da kisa

Mai gabatar da ƙara ya bayyana cewa, a lokacin da ’yan sanda suka gudanar da bincike sun gano cewar matashin ya sato doyar ce a wata gona da ke makarantar sakandare ta gwamnati a Dutse Alhaji.

Ya shaida wa kotun cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya ce ya saci doyar da nufin sayarwa amma ana cikin haka ne aka kama shi.

Ogada ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 348 da na 287 na ƙundin laifuffuka.

Alkalin kotun, Jastis Saminu Suleiman, ya yanke wa wanda ake ƙara hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata huɗu tare da biyan tarar naira 10,000.

Alkalin ya gargaɗe shi da ya guji aikata laifi mai alaƙa da hakan a nan gaba.

Leave a Reply