Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Birnin kebbi ta samu wani matashi ɗan shekara 16 Habibu Umar da laifin yin lalata da yara ƴan mata kuma aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan gyaran hali.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙara Insp. Muntari Mati, a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023, a wata ƙara mai lamba BK/538C/223, ya gabatar da Habibu Umar a gaban kotu bisa tuhuma guda ɗaya na cin zarafi ta lalata wanda ya saɓawa sashe na 263 na ƙundin laifuffukan Penal na jihar Kebbi.
Habibu ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi a gaban kotu, Alkalin Kotun Samaila Kakale Mungadi don haka ya yanke wa Habibu hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari tare da zaɓin biyan tarar naira dubu ɗari da hamsin (N150,000).
KU KUMA KARANTA: An kama yaro ɗan shekara 16 a Kebbi bayan ya yi wa ƙananan yara 2 fyaɗe
Zaku iya tuna cewa Neptune Hausa ta ruwaito cewa jami’an tsaron Masarautar Gwandu ne suka kama Habibu Umar wanda hakan ya sa aka ƙara ɗaukar mataki.
Bayan an yi masa tambayoyi na farko a Fadar Ubandoman Gwandu, daga baya aka miƙa shi ga hukumar Hisbah ta jihar Kebbi, bayan da aka yi zargin ya lalata wasu ƙananan ‘yan mata biyu masu shekaru biyar da shida a wani daji da ke tsakanin unguwar Badariya da Barikin Sojoji a Birnin kebbi a ranar 21 ga Nuwamba 2023.