Kotu a Kano ta tura matasan da suka yi yunƙurin hana zance a Unguwar Ja’en Gidan Yari

0
281
Kotu a Kano ta tura matasan da suka yi yunƙurin hana zance a Unguwar Ja'en Gidan Yari

Kotu a Kano ta tura matasan da suka yi yunƙurin hana zance a Unguwar Ja’en Gidan Yari

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Kotun shariʼar musulunci da ke Kofar Kudu a Kano karkashin mai shariʼa Shamsuddeen Ado Abdullahi Unguwar Gini ta aike da wasu matasa 2 gidan yari saboda sassara wani saurayi da ya je zance unguwar Jaʼen da adda.

Kungiyar ci gaban alʼummar Jaʼen ce ta yi karar matasan Usman Rabiʼu Usman da Aliyu Rabiʼu Usman kan zarginsu da saka dokar ta baci ta hana yin zancen saurayi da budurwa.

KU KUMA KARANTA: Hisbah a Kano za ta fara kamen masu hira da mata a cikin mota

Mai gabatar da kara, lauyar gwamnatin Kano Baristar Aliya Aminu Yargata ta karanta musu zargin amma sun musanta, sai dai ta nemi a basu wata ranar don kawo shaidu.

Lauyan wadanda ake kara Barista Jamilu Jaʼafar ya roki a ba da belinsu, amma kotun ba ta amince ba.

Kotun ta turasu gidan yari gar zuwa 22 ga watan Mayun da muke ciki, don ci gaba da shariʼa.

Leave a Reply