Hisbah a Kano za ta fara kamen masu hira da mata a cikin mota

0
102
Hisbah a Kano za ta fara kamen masu hira da mata a cikin mota

Hisbah a Kano za ta fara kamen masu hira da mata a cikin mota

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hukumar dake hani da mummunan aiki, da umarni da kyakkyawan aiki Hisbah a jihar Kano, ta sha alwashin sanya kafar wando daya da masu yin zance a mota.

Mataimakin Babban kwamandan hukumar Dr. Mujahiddeen Aminuddeen ya shaidawa Neptune Prime, cewa suna yawan samun korafi kan yadda samari da ‘yan matan ke yin lalata a cikin mota, da sunan zance.

KU KUMA KARANTA:Neman shahara: Hukumar Hisbah a Kano ta kama matashi da ya shinshini al’aurar akuya

A cewar sa hakan ne ya sanya hukumar ta shirya daukan mataki don magance wannan matsala a cikin birnin Kano da kewayen ta.

Wanda a karshe ya yi kira ga iyaye wajen sanya ido akan ‘ya’yan su, da Jan kunnen masu aikata haka domin hukumar su zatayi aiki babu sanni babu sabo.

Leave a Reply