Tanzaniya ta fi kowace ƙasa yawan dabbobi a duniya, ma’ana cewa akwai dabbobi da dama a kowace murabba’in mil a ƙasar fiye da kowace ƙasa.
Aƙalla akwai killatattun namun daji kimanin miliyan huɗu, Tanzaniya ta kasance bigire na mafi yawan dabbobi, inda ake samun dabbobi iri daban-daban da ba a ko’ina ake da su ba.
KU KUMA KARANTA:Birnin Ismailiyaya sanya Masar a matsayi na shida a duniya wajen samar da Mangwaro
Bugu da ƙari, gandun dajin Serengeti da ke ƙasar ya kasance a matsayi na huɗu a cikin jerin gandun daji waɗanda aka fi ziyarta a duniya a karo na huɗu a jere, na shekarar 2022.
Mutane daga sassa daban-daban na duniya kan ziyarci wurin domin yawon buɗe ido.