Adadin mutanen da aka kashe a jerin hare-haren da ‘yan bindiga suka kai jihar Filato da ke tsakiyar Nijeriya ya ƙaru zuwa kusan 200, kamar yadda hukumomi suka bayyana ranar Laraba, a yayin da aka soma binne waɗanda suka mutu.
Wasu ‘yan bindiga da kawo yanzu ba a san ko su wane ne ba sun ƙaddamar da jerin hare-hare a ƙauyuka kusan ashirin a jihar ta Filato ranar Asabar da maraice da kuma Talata da safe.
Tun da fari, hukumomi sun ce mutum 163 ne suka mutu a hare-haren da aka kai a ƙananan hukumomin Barkin Ladi da Bokkos.
Sai dai yayin da mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya kai ziyara a jihar ta Filato ranar Laraba, shugaban ƙaramar hukumar Bokkos Monday Kassah ya ce mutum 148 aka kashe a yankinsa.
KU KUMA KARANTA: Tinubu ya ba da umarnin cafko waɗanda suka kashe mutane 115 a Filato
Kazalika an kashe mutum aƙalla 50 a ƙauyuka daban-daban na ƙaramar hukumar Barkin Ladi, a cewar Dickson Chollom, wani ɗan majalisar dokokin jihar daga yankin.
“Muna rokonku da ku guji raba kawuna da kiyayya ga junanku, a yayin da muke ƙoƙarin ganin an yi adalci domin samar da zaman lafiya,” in ji Kashim Shettima a yayin da ya gana da jami’an gwamnati da sarakuna da kuma mazauna yankunan.
Ana fargabar cewa alkaluman mutanen da suka mutu ka iya ƙaruwa domin kuwa har yanzu akwai waɗanda suka ɓata, a cewar Kassah a hira da kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Talata, inda ya ƙara da cewa an jikkata mutum 500 sannan an raba dubbai da gidajensu.
An binne mutane da dama ranar Talata, inda mataimakin shugaban majami’ar Church of Christ in Nations, Timothy Nuwan, ya ce waɗanda aka binne sun kai 150.
“An kashe mutane da dama, wasu an yanka su kamar dabbobi, yayin da aka ƙona wasu a cikin gidajensu da kuma a waje,” in ji shi.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ranar Talata ya yi tir da hare-haren sannan ya umarci “jami’an tsaro su yi gaggawar shiga yankuna da kuma kama waɗanda suka aikata laifin”.
Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya yi ƙira “a haɗa gwiwa domin gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen-aiki”.