Kalaman wasu jami’an gwamnatin Najeriya kan matatar man Ɗangote tamkar kwancewa ƙasar zani a kasuwa ne – Masana

0
80
Kalaman wasu jami’an gwamnatin Najeriya kan matatar man Ɗangote tamkar kwancewa ƙasar zani a kasuwa ne – Masana

Kalaman wasu jami’an gwamnatin Najeriya kan matatar man Ɗangote tamkar kwancewa ƙasar zani a kasuwa ne – Masana

Masana tattalin arziƙi a Najeriya na ci gaba da yin fashin baƙi kan tasirin taƙaddamar da ke wakana tsakanin kamfanin tace man Ɗangote da hukumar kula da cinikayyar mai ta Najeriya. Matatar man ta Ɗangote ta ce a watan Agusta za ta fara fitar da fetur ɗin da ta tace a kasuwannin ƙasar.

A ranar 22 ga watan Mayu na shekarar 2023 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a wancan lokacin, gabanin miƙa mulki ga sabon shugaba ya ƙaddamar da matatar man Ɗangote da ke unguwar Lekki a birnin Legas.

Matatar da ta laƙume biliyoyin dalar Amurka wajen gina ta na da ƙarfin sarrafa gangar ɗanyen mai 650,000 a kowace rana, bayan haka za ta samar da guraban ayyukan yi ga dubban ‘yan Najeriya.

Dokoki da ƙa’idojin sarrafa albarkatun mai na Najeriya, sun yi tanadin cewa tilas ne kamfanonin da ke aikin haƙar ɗanyen mai a ƙasar su samar da shi ga matatun cikin gida kafin su saida wa na ƙetare.

Sai dai mahukuntan matatar ta Ɗangote na kokawa kan rashin samun ɗanyen man da su ke buƙata daga cikin gida.

“Abin da ke faruwa a yanzu shi ne, ana haƙo man ya fita, mu kuma muna zuwa wata ƙasar mu sayo irinsa a kawo shi Najeriya don a tace, a cewar Alhaji Rabi’u Abdullahi, babban jami’in cinikayya na rukunin kamfanonin Ɗangote.

Ya ƙara da cewa, a watan Satumba da ke tafe, su na buƙatar ƙago 15 na ɗanyen mai amma ƙago 5 kaɗai za su iya samu, “ka ga dole ne mu je mu nemo sauran ragowar a cewarsa.

Yayin matatar ɗanyen man ta Ɗangote ke kokawa kan rashin samun isasshen ɗanyen mai domin sarrafawa, a baya-bayan nan an ji shugaban hukumar kula da cinikayyar albarkatun mai ta Najeriya Alhaji Faruk Ahmed na aibata man da matatar ta Ɗangote ke tacewa, yana mai cewa ba shi da nagartar da ta dace, al’amarin da mahukuntan matatar man suka musanta.

KU KUMA KARANTA:Ƙaramin Ministan Man Fetur na neman sasanta NNPC da Ɗangote

Masana harkokin tattalin arziƙi na fashin baƙi game da illolin kalaman shugaban hukumar kula da cinikayyar albarkatun mai ta Najeriya ga makomar tattalin arziƙin Najeriya.

“Saboda irin waɗannan kalaman, yanzu zai yi wuya wani ya zo Najeriya ya zuba hannun jari, idan ma da gaske ne to kamata ya yi a sanar da gwamnati, a cewar Dakta Abdulsalam Ƙani, malami a fannin koyar da harkokin tattalin arziƙi a jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano. Ya ƙara da cewa furta irin waɗannan kalaman tamkar kwancewa ƙasar zani a kasuwa ne.

Yayin da matatar ta Ɗangote ke fama da ƙalubale da hukumomin Najeriya, mahukuntan kamfanin sun ce a watan Agusta fetur ɗin da matatar ke tacewa zai bayyana a kasuwannin ƙasar.

Leave a Reply