Jirgi mai sauƙar ungulu ɗauke da shugaban ƙasar Iran Ra’isi, ya faɗi
Daga Ibraheem El-Tafseer
Ministan harkokin cikin gidan ƙasar Iran Ahmad Vahidi ya tabbatar da cewa wani jirgin sama mai sauƙar Ungulu ɗauke da shugaban ƙasar Ebrahim Raeisi ta faɗi a birnin Jolfa da ke lardin Gabashin Azarbaijan na arewa maso yammacin ƙasar Iran.
Jirgin mai sauƙar Ungulun na jigilar shugaban ƙasar Raisi, da ministan harkokin wajen ƙasar Hossein Amir-Abdollahian, da gwamnan Azarbaijan ta gabas, Malek Rahmati, da wasu fasinjoji da dama, a lokacin da suka gamu da matsala, inda aka tilasta masa yin “sauƙar gaggawa” a kusa da Jolfa, wani birni mai iyaka da ƙasar Azarbaijan.
Lamarin ya faru ne a dajin Dizmar da ke tsakanin garuruwan Varzaqan da Jolfa.
KU KUMA KARANTA: Mayaƙan Houthi sun kai wa jirgin ruwan Amurka hari a Bahar Maliya
Bayan sa’a ɗaya da faruwar lamarin, ƙungiyoyin agaji sun isa yankin inda suka fara gudanar da bincike.
Tawagar ceto ta mutum 20 aka tura yankin, amma saboda tsananin gurɓatar yanayi, musamman hazo, aikin bincike da ceto zai ɗauki lokaci, in ji hukumomi.
Haka nan na’urori marasa matuƙa suna taimakawa da aikin gaggawa wajen binciken.
Wasu jirage masu sauƙar ungulu guda biyu ɗauke da wasu ministoci da jami’ai sun isa wurin lafiya.
Shugaba Raisi yana dawowa ne daga bikin ƙaddamar da madatsar ruwa a kogin Aras tare da shugaban ƙasar Azabaijan Ilham Aliyev.