Jinin Nasrallah ba zai tafi a banza ba, Isra’ila za ta ɗanɗana kuɗarta – Khamenei

0
79
Jinin Nasrallah ba zai tafi a banza ba, Isra'ila za ta ɗanɗana kuɗarta - Khamenei

Jinin Nasrallah ba zai tafi a banza ba, Isra’ila za ta ɗanɗana kuɗarta – Khamenei

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jagoran addini na ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce jinin jagoran Hezbollah, Sayyid Hassan Nasrallah da Isra’ila ta kashe ba zai tafi a banza ba.

Ya ce an ayyana zaman makoki na kwanaki biyar a faɗin ƙasar.

Ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan jagoran Hezbollah, Hassan Nasrallah da aka kashe.

Khamenei ya kuma jajantawa sauran ƙasashen Musulmi kan kisan na shugaban ƙungiyar.

KU KUMA KARANTA:Isra’ila ta kashe shugaban Hizbullah na Lebanon

Ya ce an kashe Nasrallah ne a lokacin da ya ke shirin kare marasa galihu na yankunan kudancin birnin Beirut da kuma gidajensu da aka lalata, da kuma rayuka masu daraja da aka rasa.

“Ba za mu gajiya ba, za mu mayar da martani mai zafi. Isra’ila za ta ɗanɗana kuɗarta,” in ji Ayatollah.

Jagoran addinin na Iran ya ce duk da cewa an yi rashin “fitaccen mutum mai iko” kuma Lebanon ta rasa “shugaba mara misaltuwa”, amma Hezbollah za ta ƙara ƙarfi.

Leave a Reply