Jihar Kano ce kan gaba a yawan masu cutar mashaƙo a Najeriya

Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce cutar mashaƙo (diphtheria) ta kashe mutum 80 a ƙasar daga watan Mayu zuwa Yunin bana.

A rahoton da hukumar ta fitar ta ce yanzu mutum 836 suka harbu da cutar kuma jihar Kano ce ta fi yawan waɗanda suka kamu da ke da mutum 819.

Hukumar ta ce alƙaluman sun shafi ƙananan hukumomi 33 na jihohi bakwai da suka haɗa da Yobe da Katsina da Sakkwato, Zamfara da Kaduna da kuma Abuja.

Ko a makon nan an bayar da rahoton mutuwar yara kusan 10 sakamakon cutar a jihar Kaduna.

KU KUMA KARANTA: Cutar mashaƙo ta kashe mutane uku, bakwai suna kwance a Asibiti a Kaduna

Tsohon shugaban hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Najeriyar Farfesa Abdussalam Nasidi, ya shaida wa BBC Hausa cewa halin da aka tsinci kai a ciki abun tashin hankali ne, ba na wasa ba.

Ya ce dole ne a tashi a ɗauki mataki, idan kuwa ba haka ba za a ji kunya.

”Ina mamaki ƙwarai, tun da bai kamata a ce ana yi wa yara rigakafin wannan cuta tun farko amma kuma ana samunta ba, abun ma da muke gani da ke tabbatar mana da cewa an gaza ne wajen yin rigakafin ko kuma wasu ba sa kai ‘ya’yansu a musu rigakafin shi ne kaso 80 ba a musu rigakafin ba.”

Ya ce wannan babbar gazawa ce da ke nuna ya kamata gwamnati da hukumomi su tashi su yi wa kansu ƙiyamallaili.

Farfesa Abdussalam Nasidi, ya ƙara da cewa a halin da ake ciki, idan har mutum ya kamu da cutar to ba lallai ne rigakafin ya yi aiki a kansa ba, ballantana da a yanzu haka ana fama da ƙarancin rigakafin shi kansa.

Yadda cutar ke kama mutum
Masanin ya bayyana wa manema labarai cewa cutar mashaƙon, na kama maƙogwaro ne, ta hana mutum sakat, ta shaƙe numfashi.

Ya ce: ”Idan ta kama mutum za ta riƙe masa wuya kamar an shaƙe ka, idan ta kama yaro idan ba Allah ne Ya kiyaye ba a gaban iyayensa za a rasa shi, don haka babban barazana ce”

Likitoci sun ce hanya ɗaya ta kauce wa kamuwa da cutar mashaƙo ga manya da ƙananan yara ita ce yin allura saboda za ta kashe ƙwayoyin cutar da ke jikin mutum.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *