Janyewar Kwamishinan ‘yansanda daga bikin tunawa da ranar ‘yancin-kai raini ne ga Gwamna – In ji Antoni Janar na Kano
Daga Jameel Lawan Yakasai
Antoni Janar na Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, AbdulKarim Maude (SAN), ya bayyana cewa janyewar rundunar ƴan sanda daga halartar bikin Ranar ‘Yancin Kai ta ƙasa ta zama barazana ga tsaro tare da ƙara haifar da tashin hankali wanda ba a buƙata a jihar.
Maude ya zargi Kwamishinan ‘Yanwanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, da take hakkin Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayinsa na Babban Jami’in Tsaron jihar, bisa abin da ya kira “raina ikon da doka ta tanada masa.”
Gwamna Yusuf ya riga ya bayyana rashin amincewarsa da Bakori a matsayin Kwamishinan ‘Yansanda na jihar, inda ya nemi a cire shi nan take bayan da jami’an ‘yansanda suka janye daga halartar bikin ranar ‘yancin kai da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha.
Yayin da yake mayar da martani kan lamarin, sabon Kwamishinan Shari’a ya bayyana cewa Kwamishinan ‘Yansanda na Kano ya karya ikon zartarwa na Gwamna kuma ya bar shi cikin haɗarin tsaro.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya canza kwamishinan shari’a
Babban Lauyan ya tunatar da cewa Kwamishinan ‘Yansanda na ƙarƙashin umarnin doka na Gwamna, musamman a al’amuran da suka shafi tsaro da zaman lafiya, sai dai idan akwai umarni kai tsaye daga Shugaban Ƙasa.
Maude (SAN) ya bayyana cewa CP Bakori ya gaza cika nauyin amana tsakanin Gwamna da Sufeton Ƴansanda na Ƙasa (IGP) yayin bikin ranar ‘yancin kai.
Duk da cewa Kwamishinan Shari’a ya ambaci sashi na 214(4) na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa, wanda ke tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda ta Najeriya tana da tsarin tsakiya, ya kuma jaddada sashi na 215 wanda ke bai wa gwamnoni ikon bayar da sahihin umarni ga kwamishinan ‘yansanda don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihohinsu.









