Jam’iyyar PDP ta dakatar da sakatarenta da wasu magoya bayan Wike
Rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar adawa ta PDP ya dauki sabon salo bayan da aka dakatar da Sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu manyan jami’an jam’iyyar da ake ganin magoya bayan Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ne, a ranar Asabar.
Mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ne ya sanar da dakatarwar bayan wani dogon zama da kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) ya gudanar a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja.
Ologunagba ya bayyana sunayen sauran wadanda aka dakatar da su da suka hada da Mai Ba da Shawara na Kasa kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Ayyuka na Kasa, Umar Bature; da Mataimakin Mai Ba da Shawara kan Harkokin Shari’a na Kasa.
Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa wadanda abin ya shafa — wadanda ake ganin dukkansu magoya bayan Wike ne — sun daina halartar tarukan shugabancin Jam’iyyar tun wani lokaci da ya gabata.
KU KUMA KARANTA: Kotu ta tsige ɗan majalisar Zamfara saboda sauya sheƙa daga PDP zuwa APC
An dakatar da su na tsawon wata guda, tare da mika batunsu ga Kwamitin Ladabtarwa na jam’iyyar domin daukar mataki na gaba.
Wannan lamari ya faru ne kwana daya bayan wata kotu a Abuja ta hana PDP gudanar da babban taronta (National Convention) da aka shirya yi a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 da 16 ga Nuwamba, 2025.
Sai dai PDP ta bayyana cewa za ta daukaka kara kan hukuncin kotun, tana mai jaddada cewa hukuncin ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryenta na taron ba.
Rashin jituwa a cikin jam’iyyar na daga cikin dalilan da suka sa aka shigar da karar da ke kalubalantar gudanar da babban taron.









