Jam’iyyar NNPP a Kano ta yi watsi da sakamakon zaɓen Tsanyanwa/Ghari

0
301
Jam'iyyar NNPP a Kano ta yi watsi da sakamakon zaɓen Tsanyanwa/Ghari
Dakta Hashim Dungurawa, shugaban jam'iyyar NNPP na Kano

Jam’iyyar NNPP a Kano ta yi watsi da sakamakon zaɓen Tsanyanwa/Ghari

Daga Jameel Lawan Yakasai

Jam’iyyar NNPP a Kano ta yi watsi da sakamakon zaben Dan Majalisar Dokoki na Ghari da Tsanyawa wanda ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaben.

Shugaban jam’iyyar Dr. Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da ya kira a ofishinsa.

KU KUMA KARANTA: Ko a mafarki jam’iyar APC ba za ta iya lashe zaɓe a Kano ba – Shugaban jam’iyar NNPP na Osun

Yace sun ki amincewa da sakamakon zaben ne saboda yadda hukumar zabe mai zaman kanta taki bayyana sakamakon zaben a mazabun da aka Kada kuri’u wanda hakan ya bawa wasu yan siyasa damar hada baki da Hukumar zaben wanda ya kai ga soke kuri’un da aka Kada a mazabu 10 da NNPP take da rinjaye.

Yace bisa dokar zabe, kowane baturan zabe shi ke da alhakin soke duk kuri’ar da ta lalace a mazabar da ya jagoranta, ba alhaki ne na shedkwatar hukumar zabe ba.

Yace Jam’iyyar NNPP zata dauki matakan da suka dace domin tabbatar da adalci ga al’umar Tsanyawa da Ghari da nufin tabbatar musu da abinda suka zaba.

Leave a Reply