Jam’iyyar ADC ta yi zargin INEC ta jefa ta cikin rikici
Daga Jameel Lawan Yakasai
Jam’iyyar adawa ta ADC ta zargi INEC da yunkurin sake jefa ta cikin rikici bayan amincewa da shugabancinta da hukumar Zaben ta yi.
ADC ta musanta wasu rahotannin da ke cewa hukumar INEC ta amince da shugabancin jam’iyyar na jihohi in da ta ce hakan yunƙuri ne na kawo da yamutsi a tsakanin ƴa’ƴanta.
KU KUMA KARANTA: Ku daina takurawa El-Rufai, ku mai da hankali kan ‘yanbindiga – Jam’iyar ADC ga ‘yansanda
Jam’iyyar ta ce ita ke da alhakin mika sunayen shugabanninta na jihohi ga INEC, kuma har yanzu bata kammala aikin tattara sunayen ba, balle ace an amince da su.









