Jam’iyar Republican ta tsayar da Donald Trump takarar shugaban ƙasa karo na uku

0
41
Jam'iyar Republican ta tsayar da Donald Trump takarar shugaban ƙasa karo na uku

Jam’iyar Republican ta tsayar da Donald Trump takarar shugaban ƙasa karo na uku

Jam’iyar Republican ta tsayar da tsohon Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump a matsayin ɗan takararta a zaɓen Shugaban ƙasar da za a gudanar a watan Nuwamba wannan shekarar.

Kwanaki biyar bayan ya tsallake rijiya da baya daga yunƙurin halaka shi, Shugaba Donald Trump ɗauke da bandeji a jikin shi ya yi jawabi ga babban taron ƙasa na jam’iyar Republican a ranar Alhamis, inda ya karɓi zaɓen da aka yi mishi na ɗan takarar shugaban ƙasa, ya kuma gabatar da jawabin da ya fuskanci batun haɗin kan jam’iyar shi da kuma haɗin kan ƙasa, a fafutukar da ya ke yi na neman shiga fadar white House a karo na uku.

Tsohon shugaban mai shekaru 78 a duniya, da ya yi fice wajen caccakar abokan hamayarsa na siyasa a jam’iyun, ya yi alƙawarin saƙon tausasawa bisa raɗin kan shi kan haɗin kai, bayan da tsallake rijiya da baya.

Jawabin na Trump shi ya kai ga cikar ƙarshen gagarumin taron gangamin kwanaki huɗu da jam’iyar ta Republican ta gudanar da ya tattaro dubban ‘yan fafutukar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya da zaɓaɓɓun jami’ai zuwa jihar raba gardama ta Wisconsin, yayin da masu kaɗa ƙuri’a ke jinjina yadda za su kaɗa ƙuri’ar su a zaɓen da zai gabatar da ‘yan takara biyu da ba su da wani farin jinin azo a gani. To sai dai a ƙasa da watanni huɗun da su ka rage aje ga takarar, manyan sauye sauye na iya faruwa a takarar, ko ma ace da wuya hakan bai faru ba.

KU KUMA KARANTA:Trump yana jinya a asibiti bayan da aka ji masa rauni wajen yaƙin neman zaɓe

Bayyanar ta Trump ta zo a lokacin da Shugaban ƙasa dan Democrat Joe Biden ke fafutukar neman ganin jam’iyar shi ta tsaida shi takara, a daidai lokacin da ake ƙara samun matsin lamba da ga manyan abokan tafiya a majalisar dokokin ƙasar, da ma su ba da gudummuwa, har ma da tsohon shugaba Barak Obama, wanda ya nuna fargaba kan mai yiwuwa ya ga za sake yin nasara a zaɓe bayan rashin kataɓus ɗin shi a muhawarar da aka yi.

An ɗauki tsawon lokaci abokan hulɗa na matsa ma shugaba Biden da ya aza ƙaimi a yaƙin neman zaɓen shi. Maimakon hakan, ya sami kan shi ne a kadaice a gidan shin a gefen ruwa a Delaware, bayan gwaji ya tabbatar da ya kamu da cutar COVID-19.

A yayin da Trump da aka sani da furta duk abin da ya fito daga bakin shi, yayi alkawari cikin lallausan lafazi a daren Alhamis, maganganun da aka shirya a ranar karshe ta babban taron, an tsara fitar da nuna karfin rauni akan Biden.Shirin ya dabbaku akan karfin kunji fiye da yadda ya kasance a ranakun makon.

Gagga gaggan waɗanda su ka yi jawabi sun haɗa da shahararren ɗan kokawar nan Hulk Hogan, shugaban zakarun ‘yan dambe Dana White, da tsohon mai gabatar da shirye shirye a kafar talbijin din Fox News, Tucker Carlson. Kid Rock shine mawakin da ya cashe a wurin.

Leave a Reply