Jam’iyar PDP ta yi kira ga hukumar zaɓe ta ƙasa, da a soke zaɓen cike-gurbi da aka yi a Kano
Daga Jameel Lawan Yakasai
Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi kira da a soke zaben cike gurbi da aka gudanar a kananan hukumomin Bagwai da Shanono na kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Kano, Yusuf Ado Kibiya, ne ya bayyana haka, inda yace zaben cike yake da tashin hankali, sayen kuri’u da kuma wasu munanan dabi’u da ke lalata tsarin dimokuraɗiyya.
A cikin jawabin sa jim kaɗan bayan kammala zaben da aka gudanar ranar Asabar a Kano, Kibiya wanda ke biyayya ga tsagin tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana damuwarsa yayin da yake magana da manema labarai, inda ya ce:
“Mu a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Kano, muna nuna damuwa kan yadda aka gudanar da zaben cike gurbi na kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano a mazabar Shanono/Bagwai.”
KU KUMA KARANTA: Akwai yiyuwar nan gaba kaɗan Ganduje ya dawo jam’iyyar PDP – Sule Lamido
“Mun shiga firgici da rahotannin da ake yadawa na barazana, tada rikici, da sauran ayyuka da ke lalata tsarin dimokuraɗiyya. Yin amfani da tashin hankali ko barazanar tashin hankali domin rinjayar masu kada kuri’a, ‘yan takara ko kuma sakamakon zabe abin Allah wadai ne, dole a yi tir da shi da mafi tsananin magana,” in ji shi.
Ya ce, “Bamu yarda da irin halayen da muka gani daga wasu bangarori, waɗanda muke ganin an yi su ne da nufin karkatar da tsarin zabe domin amfanar wani ɓangare.”
“Ya zama dole a san wannan: ingantaccen zabe mai gaskiya da adalci shi ne tubalin dimokuraɗiyya ta wakilci. Muna kira ga duk hukumomi da su ɗauki mataki na gaskiya wajen kare wannan manufa da tabbatar da cewa an nuna ainihin ra’ayin jama’a ba tare da tsoro ko nuna son kai ba.”
Ya kuma jaddada cewa, “Gwamnatin Jihar Kano da shugabannin ƙasa su guji kalaman tayar da hankali da kuma ayyukan da za su iya ƙara rikici, sannan su nuna cikakkiyar jajircewa wajen gudanar da sahihin zabe na gaskiya da zaman lafiya.”
Haka kuma ya yi kira ga “Hukumomi da su gaggauta bincikar duk wani rahoton karya dokokin zabe, sannan su hukunta wadanda aka samu da laifi gwargwadon doka, domin a yi gargaɗi ga masu shirin aikata irin wannan nan gaba.”









