Jam’iyar APC ta dakatar da tsohon Gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

0
305

Jam’iyar APC ta dakatar da tsohon Gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

Jam’iyyar APC reshen Jihar Ogun ta dakatar da tsohon gwamnan jihar kuma Sanatan Ogun ta tsakiya , Gbenga Daniel, har abada bisa zargin yin ayyukan da suka saba wa jam’iyya.

Dakatarwar, wadda ta haɗa da Kunle Folarin – ɗaya daga cikin magoya bayansa – ta samu amincewar kwamitin gudanarwa na jihar bayan mazabu nasu a Shagamu sun zarge su da aikata “ayyukan adawa da jam’iyya.”

APC ta bayyana cewa an gayyaci Daniel da Folarin domin kare kansu, amma sun ki bayyana a gaban kwamitocin ladabtarwa.

KU KUMA KARANTA: Ganduje ya Ajiye mukaminsa na Shugabancin Jam’iyar APC na Ƙasa

Haka kuma jam’iyyar ta zarge su da tsoratar da ‘yan jam’iyya tare da matsa musu lamba su janye ƙorafe-ƙorafen da aka shigar a kansu.

Ana hasashen wannan mataki na iya daɗa rura rikicin siyasa tsakanin Daniel da gwamnan Ogun na yanzu, Dapo Abiodun, musamman bayan gwamnatin jihar ta sanya alamar rushewa a wasu kadarori da ake danganta da Sanatan.

Leave a Reply