Jami’ar jihar Taraba ta rage kuɗin makaranta da kashi 50

1
426

Gwamnatin jihar Taraba, ta sanar da rage kuɗin makaranta da kashi 50. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da magatakardar Jami’ar, Joseph U. Bibinu ya sanyawa hannu ya kuma fitar a ranar Laraba, 5 ga Yulin 2023.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace ɗaliban jami’ar Jos bakwai

Hakan ya biyo bayan ziyarar da gwamnan jihar, Dakta Kefas Agbu ya kai Jami’ar, inda ya bayyana batun rage kuɗin jami’ar da kashi 50.

Jami’ar ta ce za ta sake fitar da sabon kuɗin makarantar a takarda ta gaba.

Wasu bayanai sun nuna cewa; akwai ɗalibai dake biyan dubu tamanin (80) har zuwa dubu ɗari da hamsin (150), yanzu da wannan ragin hakan na nuni da cewa rabin abin da suke biya a baya za su biya.

1 COMMENT

Leave a Reply