Jami’ar European American ta karrama mawaƙi Rarara da Digirin Girmamawa
Daga Jameel Lawan Yakasai
Jami’ar European American da ke Jamhuriyar Panama ta karrama mawaƙi Dauda Kahutu Rarara da digirin digirgir bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen raya al’adu da tallafawa matasa.
KU KUMA KARANTA: Ma mallakin shafin Facebook ya cire shafin mawaƙi Rarara
Taron wanda aka gudanar a Abuja ya samu halartar gwamnoni, ministoti da sauran manyan ƴan siyasa.










