Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta yi bukin cika shekaru 63 da kafuwa
Daga Idris Umar, Zariya
A lokacin da ake bukukuwan cikar jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya shekaru 63 shugabanta ya isar da wani saƙon cewa, “Har yanzu Jami’ar ABU na riƙe da kambunta a shekaru 63 jami’ar ta Ci gaba Da zama makarantar ƙwararru a ɓangarori daban-daban a Najeriya bisa ga manufar asalinta.
Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria tana da fannoni da dama, domin ci gaba da zama makarantan kwararru mafi girma a Najeriya, bisa ga manufar asaltinta wadda take nuna muhimmancin al’umma da kuma hadin kai na kasa.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Ahmed Adamu, wanda ya bayyana hakan a yayin ganawar da ya yi da ‘yan jarida a lokacin bikin cika shekara 63 na Jami’ar a cambarsa dake jami’ar.
Ya bayyana cewa, jami’ar ABU na dauke da fiye da malamai 600, wanda shine mafi yawan kowace jami’a a Najeriya, kuma tana da hadin gwiwa da fiye da cibiyoyi 100 na kasa da kasa.
A cewar sa, ABU tana samun kiran “Jami’ar Jami’o’i,” saboda tana taimaka wa wajen kafa kusan kowace jami’a a Arewacin Najeriya, tare da fiye da daliban dinga 600,000 daga ko’ina cikin duniya.
Farfesa Adamu ya ce jami’ar ta ABU ta sami lambar yabo daga JAMB a matsayin Jami’a mafi kyawun 2025 a fannin kasa da kasa da bambance-bambancen al’umma.
Har ila yau, ABU na daya daga cikin jami’o’in guda uku a Najeriya da suka samu gurbin shiga jerin manyan jami’o’i na QS a shekarar 2025, yayin da cikin shekarun da suka gabata, Jami’ar ta samu tallafin cibiyoyin kwarewa guda 3 na Bankin Duniya da suka kai kimanin dala miliyan 15, wanda shi ne mafi yawa da kuma mafi girma a kowace jami’a a Najeriya.
KU KUMA KARANTA: Farfesa Adamu Ahmed ya zama shugaban jami’ar Ahmadu Bello na 14
A shekarar 2025, jami’ar ta kuma samu tallafin Euro miliyan 5 daga shirin Horizon don gudanar da aikin AI na “multiplex” wanda zai haɓaka ingancin binciken cututtukan ƙwayoyin halitta masu yaduwa ta hanyar amfani da na’urar hangen nesa ta AI.
Shugaban jami’ar ya kara da cewa, daliban su sun lashe kyaututtuka da dama a fannin ICT a matakin ƙasa da ƙasa, ciki har da gasa ta duniya ta Huawei, wanda hakan ya nuna fasaha, kirkira, da gasa a matakin duniya.
A kan kalubalen da Jami’ar ke fuskanta, Farfesa Ahmed Adamu ya bayyana cewa babban kalubalen da ke fuskantar su shi ne matsalar rashin isasshen kudi wanda ke shafar yadda ake gudanar da harkokin jami’ar da kuma rashin kwararrun ma’aikata da ke tafiya neman damar aiki a cikin gida da kuma kasashen waje.
Shugaban jami’ar ya nuna damuwa kan tsohon kayan aikin da ake amfani da su a jami’ar, wanda ke bukatar gyara gaggawa, da kuma matsalar rashin kyakkyawan albashi wanda ke rage kwarin gwiwar ma’aikata.
A ɓangaren tsaro kuwa ta tabbatar da cewa jami’ar na aiki kafada da kafada da cibiyoyin tsaro dake fadin kasar don ƙare rayukan ɗalubai da ma’aikatan jami’ar.
Karshe yayi fatan Alheri ga shugaban kasan Najeriya da Gwamnan jihar Kaduna bisa gudummawar da suke baiwa jami’ar a ɓangarori da dama.









