Jami’an tsaro sun far wa hedikwatar NLC a Abuja
Daga Ali Sanni
Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bayyana cewa jami’an tsaro ɗauke da muggan makamai sun yi dirar-mikiya a hedikwatarta da ke Abuja wato Labour House.
Ƙungiyar tace ma’aikatan sun afkawa babbar ma’aikatar da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare.
Inda suka ɓalle majiyar littatafai da takardun ƙungiyar dake hawa na biyu a ginin ma’aikatar inda suka ɗauke ɗaruwan littatafai cewar mai magana da yawun ƙungiyar Benson Upah.
Ma’aikatan da suka afkawa ma’aikatar na iƙirarin neman wasu mahimman takaddu da suga bada gudummawar zanga-zangar tsadar rayuwa da ake yi a faɗin ƙasar.
Kawo yanzu Ƙungiyar ta ƙwadago har yanzu bata iya ƙayyade iya abunda jami’an tsaron suka ɗebe ba.
KU KUMA KARANTA: An kama sojan da ya harbe mai zanga-zanga a Zariya
Wannan al’amarin ya faru biyu bayan kwanaki shiga da masu zanga-zangar tsadar rayuwa a matsin tattalin arziki a Najeriya.
Kungiyar ta ƙwadago tayi tur da Allah wadai da matakin da jami’an tsaron suka ɗauka.
Inda suka ƙara da cewa ko a lokacin bakin mulki na sojojin hakan bai taɓa faruwa ba.