Jamhuriyar Nijar ta katse hulɗar soji da Amurka

0
143

A ci gaba da kwan gaba kwan baya da hulɗar Jamhuriyar Nijar da wasu ƙasashen Yamma ke yi, ƙasar da ke ƙarƙashin mulkin soji, ta yi shelar yanke hulɗar soji da Amurka.

Sanarwar da kakakin majalisar CNSP, Kanal Abdourahamane Amadou, ya gabatar a kafar talabijin mallakar gwamnati a cikin daren jiya Asabar na cewa Jamhuriyar Nijar ta tsinke hulɗar ayyukan soja da ƙasar Amurka sakamakon rashin gamsuwa da halaccin yarjejeniyar da aka fake da ita don shigo da dakarun sojan Amurka a ƙasar ta Nijar a 2012 cikin wani yanayi mai kama da tilastashi ba dan rai ya so ba.

Haka kuma rashin samun wata gudunmowar da ta dace daga Amurka a yunƙurin murƙushe matsalolin tsaron da ke sanadin rasa rayukan sojoji da al’ummar Nijar ya sa majalisar CNSP da gwamnatin riƙon ƙwarya suka umurci dakarun nan 1100 da Amurkar ta girke a sansanoni daban-daban su fice daga wannan ƙasa ba tare da ɓata lokaci ba a cewar wannan sanarwa.

Wannan sabon al’amari na zuwa ne a washegarin rangadin da wata tawagar jami’an gwamantin Amurka ta gudanar a Nijar a ƙarƙashin jagorancin mataimakiyar sakataren gwamnatin Amurka mai kula da harakokin Afrika, Molly Phee, inda suka tattauna da Fira Minista Ali Lamine Zeine da wasu muƙarraban gwamnatinsa dangane da shirin mayar da Nijar tafarkin Dimokuraɗiyya bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023. Koda yake yunƙurin ganawar Amurkawan da Janar Abdourahamane Tiani ya ci tura, lamarin da ke fayyace alamun an yi watsewar baram baram a zaman da ya haɗa jami’an ƙasashen biyu.

KU KUMA KARANTA:Shugaba Tinubu ya ba da umarnin buɗe iyakokin Najeriya da Nijar nan-take

A wani ɓangare na wannan sanarwa hukumomin na Nijer sun nuna rashin gamsuwa da abin da suka ƙira muguwar halayyar da sakatariya Molly Phee ta nuna a yayin ziyarar ta ranakun Talata, Laraba da Alhamis ɗin da suka gabata.

Hulɗa a tsakanin Nijar da ƙasashen Russia da Iran na daga cikin batutuwan da sanarwar ta hukumomin mulkin sojan Nijar ta taɓo, suna masu kare matsayin ƙasar da suka ce ta na da ‘yancin zaɓin ƙawayen da suka dace da manufofinta a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta.

Ƙasar Amurka wace ta yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yulin 2023 ta dakatar da bai wa Nijar tallafin da ta saba bayarwa a fannoni da dama, ciki har da fannin tsaro. haka kuma ta sha yin hannunka mai sanda kan dukkan wani yunƙurin ƙulla mu’amula da ƙasashe irinsu Rasha masu amfani da sojan haya a matsayin hanyar kula da sha’anin tsaro.

Leave a Reply