Iyayen ɗaliban da aka sace a jami’ar tarayya a Zamfara sun yi zanga-zanga

Iyayen ɗaliban da aka sace a Jami’ar Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a gidan gwamnatin jihar, suna neman a sako ’ya’yansu ba tare da wani sharaɗi ba.

Sun buƙaci Gwamna Dauda Lawal da jami’an tsaro su ceto ’ya’yansu da aka yi garkuwa da su tsawon kwanaki 72 ba tare da wani abu ya same su ba.

Masu zanga-zangar sun sha alwashin ci gaba da zama a gidan gwamnatin Jihar Zamfara har sai an sako ’ya’yansu.

Sun ce ’yan bindigar sun tuntuɓi wasu daga cikinsu kuma sun bayar da sharaɗin tattaunawa da gwamnatin jihar kafin sakin ɗaliban.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun ƙara sace ɗaliban jami’ar Zamfara

A ranar 22 ga watan Satumba ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da ɗaliban jami’ar kimanin 24 tare da wasu ma’aikata a jami’ar.

Sai dai an ƙubutar da ɗalibai 13 da ma’aikatan gini uku yayin da har yanzu raguwar suke tsare a hannun ’yan bindigar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *