Isra’ila ta lashi takobin kai munanan hare-hare kudancin Gaza

0
62

Firai Ministan Isra’ila ya faɗa a ranar Lahadi cewa, yuwuwar tsagaita wuta a yaƙin da ƙasarsa ke yi da mayaƙan Hamas zai jinkirta kai hari ta ƙasa ne kawai a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda ya zama mafaka ga fiye da rabin al’ummar yankin da ke fuskantar rikici.

A yayin da ake fama da matsalar jin ƙai, babbar hukumar ba da agaji ga Falasɗinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci a ɗauki matakan siyasa don daƙile yunwa a Gaza.

Masana daga ƙasashen Masar, Qatar da Amurka sun gana a birnin Doha, har ma da wakilan Isra’ila da na Hamas, kamar yadda kafafen yaɗa labaran Masar masu alaƙa da gwamnatin Masar suka bayyana, wani ƙoƙari na baya-baya da ake don ganin an cimma yarjejeniya kafin watan Ramadana mai alfarma.

Firai Minista Benjamin Netanyahu ya ce farmaƙin soji a Rafah da ke kan iyakar Gaza da Masar, zai taimaka wa Isra’ila samun “cikakkiyar nasara” cikin ‘yan makwanni akan Hamas, mayaƙan da harin da suka kai a ranar 7 ga watan Oktoba ne ya ya yi sanadiyar fara yaƙin.

Ana fargabar irin wannan farmakin zai janyo asarar rayukan fararen hula da yawa a Rafah, inda Falasɗinawa kusan miliyan 1.4, waɗanda akasarinsu ‘yan gudun hijira ne daga wasu wurare, suka tattaru.

“Ko da ba mu cimma wata yarjejeniya ba, za mu ci gaba da yin hakan,” in ji Netanyahu.

“Dole ne a yi hakan domin cikakkiyar nasara ita ce burinmu, kuma tana gab da samuwa, ba nan da watanni ba, amma nan da makonni kaɗan da zarar muka fara aikin,” abin da Netanyahu ya gaya wa CBS kenan game da kai farmaƙin ta ƙasa.

KU KUMA KARANTA:Mahara sun kashe mutane 15 a wani Coci a Burkina Faso

Mummunan ƙarancin abinci da ake fama da shi a arewacin Gaza wanda ya sa Falasɗinawa tserewa zuwa kudu “wani bala’i ne bil’adama ya janyo wanda za a iya shawo kan lamarin,” in ji Philippe Lazzarini, shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta UNRWA.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tana fuskantar ƙalubale musamman akan kai kayan agaji zuwa arewacin Gaza.

Wata majiyar Hamas ta shaida wa AFP cewa, an gabatar da wasu sabbin gyare-gyare kan batutuwan da ake taƙaddama a kai, amma Isra’ila ba ta gabatar da wata ƙwaƙƙwarar matsaya ba akan sharuɗɗan tsagaita wuta da kuma janyewa daga zirin Gaza.

Netanyahu ya yi watsi da buƙatar janye sojojinsa.

Sama da watanni huɗu da aka kwashe ana yaƙin, akan dole iyalai marasa galihu a arewacin Gaza suke neman abinci a bola saboda faɗa da warwaso sun dakatar da kai kayan agaji.

Leave a Reply