Isra’ila ta kashe mata da yara sama da 25,000 a Gaza — Pentagon

0
131

Isra’ila ta kashe mata da yara ƙanana Falasɗinawa sama da 25,000 tun ranar 7 ga watan Oktoba, in ji Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin.

“Ya haura 25,000,” Austin ya shaida wa ‘yan majalisa lokacin da aka tambaye shi a yayin zaman kwamitin kula da ayyukan soji na majalisar game da adadin mata da yara da aka kashe.

Amurka dai ta goyi bayan Isra’ila tun bayan da ta mayar da martani ga harin da Hamas ta kai wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a Zirin Gaza wanda Ma’aikatar Lafiya ta yankin da ke gaɓar teku ta ce ya kashe mutane fiye da 30,000.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar EU ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa 112

Adadin da Austin ya bayar ya yi daidai da hukumomin Falasɗinun, kuma ya zo ne yayin da Washington ke matsawa da batun a tsagaita wuta

Leave a Reply