Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 165 daga Juma’a zuwa Asabar

0
99

Aƙalla Falasɗinawa 165 Isra’ila ta kashe tare da raunata 280 a sa’o’i 24 da suka wuce, haka kuma akwai mutane da dama da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai sakamakon hare-hare da Isra’ila ta kai kan gidajen jama’a, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya da ke Gaza ta tabbatar.

“Ƴan Isra’ila masu mamaya sun yi kisan kiyashi ga iyalai 14 a Zirin Gaza, inda suka kashe mutum 165 da raunata 280 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata,” in ji ma’aikatar a wata sanarwa.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe farar hula bakwai a Gaza da Khan Younis

“Akwai mutane da dama da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai da kan tituna sakamakon masu aikin ceto sun kasa kaiwa a gare su,” in ji sanarwar.

Leave a Reply