No menu items!

Sample Page Title

Date:

Isra’ila ta kai ƙarin hare-hare a Gaza da Lebanon

Isra’ila ta ce ta kai harin ne kan wata cibiyar da ake ba da umarni da ke cikin wata makaranta.

Hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza da babban birnin ƙasar Lebanon sun kashe mutane da dama a ranar Alhamis, yayin da sojojin Isra’ila suka ce sun kai wa ‘yan ta’adda hari ne.

Jami’an lafiyar Falasɗinawa sun ce hare-haren saman na Isra’ila sun fada kan wata makaranta a Gaza da ke zama mafaka ga mutane da suka rasa muhallansu suna masu cewa mutum 27 ne suka rasa rayukansu.

Isra’ila ta ce ta kai harin ne kan wata cibiyar da ake ba da umarni da ke cikin makarantar.

KU KUMA KARANTA:Ba za mu bari Isra’ila ta kori Falasɗinawa ba – Sarkin Jordan 

A babban birnin kasar Lebanon, Isra’ila ta kai hari a wani gini da ke tsakiyar birnin, mai nisa daga inda nan ne kungiyar Hezbollah ke da karfi sosai a kudancin birnin Beirut.

Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta ce adadin wadanda suka mutu ya kai 22, yayin da 117 suka samu raunuka, amma ana fargabar za su karu yayin da masu aikin ceto suka maida hankali kan baraguzan ginin.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...